Wata Dattijuwa Ta Kira 'Yansanda Don Su Mata Girki.
Daga Asma'u Bashir Bello, Zaria
Idan da ranka ka sha Kallo wata wata dattijuwa Yar Iitaliya mai shekaru 87 ta kira ƴan sanda saboda tana jin yunwa kuma ba ta iya girki, Kuma ba tare da bata lokaci ba jami'ai biyu suka je gidanta suka shirya mata abincin dare.
Wannan abin al'ajabin ya faru a birnin Florence na ƙasar Italiya, Inda wannan dattijuwa mai shekaru 87 wadda ta kasance ita kaɗai a gida bayan mai kula da ita bai zo ba, ta kira lambar 113 wadda take daidai da lambar gaggawa ta kiwon lafiya ta Faransa domin neman taimako:
"Na gaji kuma ina jin yunwa, amma ba zan iya girki ba saboda hannuna yana ciwo." Jami'an ƴan sanda biyu daga rundunar ƴan sandan Florence sun amsa kiran, suka shiga gidanta, sannan suka shirya mata abinci.
Shin kuna ganin 'Yansandan Nijeriya zasu Iya wannan kuwa?


No comments