Ƙungiyar Editoci Ta NGE Ta Nuna Damuwarta Kan Cin Zarafin ’Yan Jarida, Ta Buƙaci Adalci Gabanin Zaɓukan 2027
Shugaban Ƙungiyar, Eze Anaba
Daga Al-Amin Ciroma
Ƙungiyar Editocin Najeriya (NGE) ta nuna damuwa kan yadda hukumomin tsaro ke ƙara cin zarafi, tsoratarwa da gurfanar da ’yan jarida a gaban kotu, tana gargaɗin cewa irin waɗannan matakai na iya kawo cikas ga ’yancin aikin jarida da kuma gudanar da aikin bisa ƙa’ida.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da su tabbatar da cewa an samar da daidaitaccen yanayi ga dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Jaridar TNL HAUSA ta ruwaito cewa waɗannan matsayi na ƙungiyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar a ƙarshen taron Kwamitin Tsare-tsare na kungiyar ta NGE da aka gudanar a Kano, ranar Juma’a, 11 ga Satumbar 2026, wadda Shugaban ƙungiyar, Eze Anaba, da Babban Sakatarenta, Onuoha Ukeh, suka sanya wa hannu.
Editocin sun nuna damuwa ta ainun kan yadda ake amfani da dokokin yaƙi da laifukan Yanar Gizo da wasu dokoki ta hanyoyin da ka iya takura wa halastaccen aikin jarida. Sun jaddada cewa ’yancin aikin jarida na daga cikin muhimman ginshiƙan dimokuraɗiyya da shugabanci nagari.
Kan haka ne, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai da kuma jama’a da su mutunta ’yancin aikin jarida, tare da yin hulɗa mai ma’ana da kafafen yaɗa labarai, maimakon barazana, tsoratarwa ko amfani da ƙarfi kan ’yan jarida da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai.
Wakilinmu ya gano cewa NGE ta shawarci mutane da ƙungiyoyin da ke da koke-koke kan kafafen yaɗa labarai da su gabatar da ƙorafinsu ga Mai Sasanta Rikicin Kafafen Yaɗa Labarai (Media Ombudsman), wanda ƙungiyar Masu Mallakar Jaridun Najeriya (NPAN), da ƙungiyat NGE, da ƙungiyar ’Yan Jaridun Najeriya (NUJ) da kuma ƙungiyar Masu Buga Jaridun Intanet na Kamfanoni (GOCOP) suka kafa tare.
Dangane da da babban zaɓen shekarar 2027 kuwa, NGE ta yi kira ga gwamnatoci da su samar da yanayi mai kyau da zai bai wa dukkan jam'iyyun siyasa da 'yan takararsu damar gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Musamman ma, ta yi kira ga hukumomi da su ba da damar sanya alamomin jam’iyyu a wuraren da doka ta amince da su, da kuma yaɗa taken kamfen, tare da roƙon INEC da sauran hukumomin da ke da hannu wajen shirye-shiryen zaɓen da su tabbatar da cewa ana yi wa dukkan jam’iyyun siyasa, ciki har da jam’iyyar da ke mulki da jam’iyyun adawa, adalci ba tare da nuna wariya ba.
Ƙungiyar, har ila yau, ta ce samar da daidaitaccen yanayi ga dukkan masu takara zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a, yarda da tsarin zaɓe da kuma mutuncin zaɓe. Ta kuma buƙaci ’yan siyasa da jam’iyyun siyasa da su mayar da hankali kan muhimman batutuwa a lokacin kamfen, su guji kalaman tunzura jama’a, sannan su bi ƙa’idojin da ke jagorantar gudanar da kamfen na siyasa.
Editocin sun kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su kiyaye mafi girman ƙa’idojin ƙwarewa da ɗa’a a aikin jarida, tare da tabbatar da adalci, rashin son rai, sahihanci da gaskiyar bayanai wajen ɗaukar rahotannin siyasa da sauran batutuwan ƙasa.
Dangane da tattalin arziki, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da take yi, tare da tabbatar da cewa jin daɗi da walwalar ’yan Najeriya sun kasance a tsakiyar manufofi da ayyukanta.
Ta nuna damuwa kan yadda yanayin manyan titunan gwamnatin tarayya a faɗin ƙasar ke ƙara lalacewa, tana mai cewa wannan hali ya jefa masu ababen hawa, matafiya da ’yan kasuwa cikin manyan matsaloli.
Saboda haka, NGE ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara kaimi wajen gyaran tituna, sake gina su da kuma gina sababbi, domin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki.
Ƙungiyar ta yaba wa hukumomin tsaron ƙasar bisa nasarorin da suka samu wajen yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga da sauran nau’o’in aikata laifuka. Sai dai ta yi kira da a ci gaba da haɗa kai da ɗorewar ƙoƙari domin cimma zaman lafiya mai ɗorewa, tsaro da haɗin kan ƙasa.
Editocin sun nuna godiyarsu ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da kuma gwamnatin jihar da al’ummar jihar baki ɗaya, bisa samar da yanayi mai kyau da ya ba da damar gudanar da taron Kwamitin Tsare-tsaren NGE, da kuma irin kyakkyawar tarbar da suka yi wa mahalarta taron.
Ƙungiyar ta sake tabbatar da cewa shugabanci nagari, jin daɗin jama’a, zaman lafiya, ci gaba da mutunta ƙa’idojin dimokuraɗiyya su ne muhimman ginshiƙan samar da al’umma mai ɗorewar zaman lafiya da wadata.


No comments