Tsawaita Wa’adin Magu A Kan Matsayin Muƙaddashin Shugaban EFCC Ya Saɓa Wa Doka -Kotun Ɗaukaka Ƙara
Daga Hadi Bawa
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa ci gaba da riƙe matsayin Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Zamba ta Ƙasa (EFCC) na tsawon lokaci da Ibrahim Magu ya yi ya saɓa wa doka.
Kotun ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da a baya ta amince da ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙarar ne ya yanke wannan hukunci a ranar Litinin, a kan ƙarar da wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya shigar. Jideobi ya ƙalubalanci ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC, bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da nadinsa a matsayin cikakken shugaban Hukumar har sau biyu.
Ƙarar ta samo asali ne daga hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta yanke a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar 4 ga Disamba, 2019.
Magu ya kasance Muƙaddashin Shugaban EFCC daga shekarar 2015 zuwa Yuli 2020, lokacin da aka dakatar da shi daga aiki.
Jideobi ya shigar da ƙarar a Babbar Kotun Tarayya a watan Maris na 2017, yana mai cewa Magu ba zai iya ci gaba da kasancewa Muƙaddashin Shugaban Hukumar ba na wani lokaci marar iyaka, musamman bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa.
A hukuncin da ta yanke a shekarar 2019, Mai Shari’a Ojukwu ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC.
Alƙalin ta ce dokar kafa EFCC, musamman sashe na 2(3), ba ta taƙaita ikon shugaban ƙasa na ci gaba da riƙe Magu a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar ba.
Ta kuma bayyana cewa akwai giɓi a cikin dokar, wanda ya bai wa tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari damar ci gaba da riƙe Magu a matsayin muƙaddashi, saboda babu wani takamaiman lokaci da doka ta ƙayyade na tsawon lokacin da mutum zai iya kasancewa a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar.
Alƙalin ta ƙara da cewa sashe na 1(2)1 na dokokin Majalisar Dattawa da mai ƙara ya yi wa kotu nuni da shi, ya shafi waɗanda aka naɗa ministoci ne kawai, kuma ba za a iya amfani da shi wajen matsayin Muƙaddashin Shugaban EFCC ba.
Kotun ta kuma ce mai ƙarar ba shi da hurumin shigar da ƙarar (locus standi).
Sai dai Jideobi, wanda bai gamsu da wannan hukunci ba, ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara.
A cikin ƙarar tasa, ya yi iƙirarin cewa shugaban EFCC yana da wa’adin shekaru huɗu ne, wanda za a iya sabunta shi sau ɗaya kawai, kuma Magu ya zarce wa’adin da doka ta tanada ba tare da samun amincewar Majalisar Dattawa ba.
Ya kuma yi gardamar cewa nadin Magu a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar ya ƙare ta hanyar aiki da doka, bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa.
Jideobi ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya, tare da amincewa da buƙatun da ya gabatar a ƙarar tasa ta farko.
Waɗanda aka kai ƙarar a Kotun Ɗaukaka Ƙara sun haɗa da Majalisar Dattawa, Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, EFCC da Ibrahim Magu.


No comments