Breaking News

Ta Gurfana A Gaban Kotu Saboda Amfani Da Kalaman Batsa A Tallace-Tallace

Daga Hadi Bawa 

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta gurfanar da mai kamfanin Kausar Unique Empire Ltd, wadda aka fi sani da Hajiyar ‘Back to Back’, da wasu masu sana’ar sayar da magunguna a gaban kotu.

An gurfanar da mutanen ne bisa zargin yin amfani da kalaman batsa wajen tallata hajojinsu da kuma wasu laifukan da hukumar ta ce sun saɓa wa dokokinta.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 29 ga Satumba, 2026.

A cewar sanarwar, waɗanda aka gurfanar sun haɗa da mamallakan Kausar Unique Empire Ltd da Shufa’u Islamic Medicine. 

Hukumar ta kuma zarge su da rashin yin rajista da ita, tare da rashin gabatar da tallace-tallacen da suke shirin yaɗawa domin tantancewa da samun sahalewa kafin a fara watsa su.
Baya ga waɗannan, hukumar ta ce ta gurfanar da wasu mutane 20 masu sana’ar buga takardu da sauran kayan talla, bisa zargin rashin yin rajista da hukumar da kuma aikata wasu abubuwan da ake zargin sun saɓa wa dokokinta da ƙa’idojinta.

Daraktan Ɗab’i na Hukumar, Alhaji Abubakar Zakari Garin Babba, ya buƙaci masu hulɗa da hukumar da su tabbatar da cewa suna bin dokoki da ƙa’idojin da aka gindaya, domin kauce wa fuskantar matakan shari’a.

Hukumar ta kuma jaddada cewa masu tallace-tallace da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa bayanai su tabbatar da cewa abubuwan da suke son yaɗawa sun cika dukkan ƙa’idojin da suka dace kafin a fara watsa su.

A baya Hukumar ta rufe shagon Kausar Unique Empire Ltd da ke Sharaɗa bisa zargin amfani da zane-zane na batsa a tallace-tallacen da ke gabatarwa a social media.

No comments