Sojoji Sun Yi Wa ’Yan Ta’adda Ƙofar Rago A Katsina, Sun Kuɓutar Da Mutane 14
Daga Hadi Bawa
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun kama wasu mutane uku da ake zargin masu kai wa ’yan ta’adda kayan aiki da kuɗi ne, tare da ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Wata sanarwa da TNL HAUSA ta samu wacce Jami’in Yaɗa Labarai na Rundanar FANSAN YAMMA Laftanar Kanal Aliyu Ɗanja ya sanya wa hannu, kamar yadda aka wallafa ta a shafin rundunar na Facebook.
Sanarwar ta ce an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 24 ga Satumba, 2026, bayan dakarun Sector 2 sun tare su a lokacin da suke tafiya a kan babur a yankin.
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa ana zargin mutanen da safarar Naira miliyan 2.7, waɗanda ake kyautata zaton kuɗin fansa ne, tare da wayoyin hannu guda uku, domin kai su ga wani babban ɗan ta’adda ta hannun wasu masu shiga tsakani.
A wani samame na daban da aka gudanar a ranar 25 ga Satumba, dakarun sun samu sahihan bayanan sirri kan motsin ’yan ta’adda a Faskari, inda suka yi masu kwanton ɓauna suka yi ram da su.
Sanarwar ta ce hakan ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa, yayin da dakarun suka ƙwato bindiga ƙirar AK-47, harsasai 30 da kuma babur.
Haka kuma, a wannan rana, dakarun da ke gudanar da sintiri na yau da kullum sun ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka ƙunshi maza 12 da mata biyu.
An ce ’yan ta’addan sun yi garkuwa da mutanen ne daga ƙauyukan Unguwar Miko da Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari, amma suka tsere suka bar su bayan sun hangi dakarun da ke tunkaro su.
Daga bisani, an miƙa waɗanda aka ceto ga hukumomin ƙaramar hukumar Faskari domin ɗaukar matakan da suka dace na kula da lafiyarsu.
Rundunar ta ce waɗannan ayyuka sun sake tabbatar da ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, da kuma taƙaita ayyukan ’yan ta’adda da sauran miyagu a faɗin yankin da ke ƙarƙashin kulawar rundunar haɗin gwiwa.
Ta kuma yaba wa dakarun bisa ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da tsaro, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa kan duk wani abin da suke zargin yana da alaƙa da ayyukan ta’addanci ko sauran laifuka a cikin al’ummominsu.


No comments