Breaking News

Sojoji Sun Sha Alwashin Ceto Malaman Addini Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Daga Hadi Bawa 

Rundunar Sojin Najeriya ta lashi takobin ceto wasu malaman addinin Musulunci shida da aka yi garkuwa da su a jihar Zamfara.

TNL HAUSA ta samu rahoton cewa, rundunar ta musanta rahotannin da ke cewa an yi garkuwa da malaman ne a gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, da ke ƙaramar hukumar Talata Mafara.

Wata majiya ta shaida wa Wakilinmu limaman da aka sace sun haɗa da; Liman Yahuza na masallacin Juma'a na Dogon Maɗacci da Malam Magawata Abdullahi Na'ibin Limamin Juma'a na Dogon Maɗacci da Liman Shehu Dakko da Liman Bala Fagon da Malam Na'ibi Tasi'u Tungar Nagudai.

Rundunar ta ce an sace malaman ne a lokacin da suke kan hanya a yankin dajin Sububu da ke ƙaramar hukumar Bakura zuwa Talata Mafara. 

A sanarwa da Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ɓangaren 8, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar ranar Lahadi yana bayyana cewa, rahotannin da ke cewa an sace malaman a gidan Sanata Yari ba gaskiya ba ne. 

Rundunar ta ce bayanan sirri sun tabbatar da cewa an sace malaman ne yayin da suke tafiya daga yankin dajin Sububu da ke Bakura zuwa Talata Mafara.

A cewar rahoton Daily Trust, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da limaman Juma’a shida a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar taron addu’a ta musamman da aka shirya domin neman zaman lafiya da samun nasarar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027. 

An ce lamarin ya faru ne kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri, a Gidan Suleiman Bature da ke dajin Gonar Sarkin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ma ta tabbatar da faruwar lamarin, inda kakakinta, DSP Yazid Abubakar, ya ce an sace limamai shida, kuma jami’an tsaro sun ƙara zage damtse wajen ceto su.

Rundunar Sojin ta ce dakarunta, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro da hanyoyin samun bayanan sirri daga al’umma, suna ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da waɗanda aka sace. 

Ta buƙaci jama’a su yi watsi da rahotannin ƙanzon kurege da ba a tantance ba, su ci gaba kasancewa cikin natsuwa da taka-tsantsan, tare da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gudanar da aikin ceto.

No comments