Breaking News

Shin Akwai Siyasa A Tsarewar Da Kotu Ta Yi Wa ’Yar TikTok Khadija 'Yar Lele A Kano?


Daga Hadi Bawa

Wata kotu ta ingiza ƙeyar fitacciyar 'yar TikTok, Khadija Muhammad 'Yar Lele, gidan gyaran hali a Kano, bayan an gurfanar da ita bisa zargin ɓata suna da kuma cin mutuncin wani ɗan siyasa a jihar.

An gurfanar da Khadija ne a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Post Office, a ƙaramar hukumar Nassarawa da ke ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Garba Malafa, inda ’yan sanda suka shigar da tuhume-tuhumen da ake mata.

Bayan karanta mata tuhume-tuhumen, Khadija ta musanta zargin da ake mata, amma sai dai mai shari'ar ya aika ta kurkuku kafin zuwan ranar da za a ci gaba da sauraron ƙarar.

Mai gabatar da ƙara, Barista Awaisu Sani Lawan, ya roƙi kotun da ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar domin bai wa ɓangaren masu gabatar da ƙara damar gabatar da shaidu a zaman da za a yi na gaba.
Bayan sauraron ɓangarorin biyu, kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Khadija a gidan gyaran hali zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026, domin sake gurfanar da ita da ci gaba da sauraron shari’ar.

Tun da farko dai, an zargi Khadija da wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, inda ake zargin ta yi kalaman ɓatanci da cin mutunci ga mai ƙarar, MD Hassan, wanda rahotanni suka bayyana a matsayin ɗan siyasa daga ƙaramar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.

Rahotannin sun ce a cikin bidiyon, ana zargin Khadija da kiran ɗan siyasar da wata kalmar ɓatanci, wadda ta jawo aka kai lamarin gaban kotu. 

Bisa dokokin Nijeriya duk wanda ake tuhuma ba mai laifi ba ne, har kotu ta tabbatar da zargin da ake masa.

Wasu lauyoyi da TNL HAUSA ta tuntuɓa kan wannan dambarwa, sun tabbatar da cewa laifin da ake tuhumar Khadija da shi za a iya bayar da belinta kafin ranar da za a dawo kotu.

Wasu makusantan wanda ake ƙara na sun bayyana mana cewa akwai yiwuwar za a sasanta lamarin a wajen kotu zuwa gobe Litinin.

No comments