Dattijuwa Mai Shekara 81 Da Ta Sauke Alƙur’ani Bayan Shekaru 40 Ta Zama Abar Misali
Daga Hadi Bawa
Jama'a na ci gaba da tururuwa zuwa gidan wata dattijuwa mai shekaru 81 domin taya ta murnar kammala sauke Alƙur’ani Mai Girma bayan ta shafe kusan shekaru 40 tana karatu da nazarin Littafin Allah.
Hajiya Sa’adatu Nuhu Waziri da ke zaune a unguwar Tudun Wazirci da ke cikin birnin Kano, ta sa ’ya’ya da jikokinta cikin farin ciki da jin daɗi sakamakon wannan gagarumar nasarar da ta samu a rayuwa.
Hajiya Sa’adatu, wacce aka fi sani da Hajiya Tayaki, ta shafe tsakanin shekaru 30 zuwa 40 tana karatun Alƙur’ani a makarantar da ke cikin gidan Wazirin Kano, kamar yadda makusantanta suka bayyana.
Tafiyar da ta ɗauki tsawon shekaru da dama ta zama abin koyi wajen nuna haƙuri, jajircewa da dagewa wajen neman ilimin addini, musamman ganin cewa ta kammala karatun ne tana da shekaru 81, ta zama abar misali a tsakanin jama'a.
A yayin bikin, an gudanar da addu’o’i tare da yi wa Hajiya Sa’adatu fatan ƙarin lafiya da tsawon rai, da kuma addu’ar Allah Ya sanya Alƙur’ani ya zama haske, shiriya da albarka a rayuwarta.


No comments