Sabuwar Taƙaddamar Ta Kunno Kai Kan Rahoton Ɓatanci Ga Annabi (S) A Kano
Daga Hadi Bawa
Wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai kan rahoton Majalisar Shura ta Jihar Kano dangane da binciken da ta gudanar kan zargin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) da ake dangantawa da Sheikh Lawan Triumph.
Lamarin ya sake ɗaukar hankalin jama’a ne bayan Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa har yanzu ba a miƙa masa rahoton binciken ba, abin da ya ce ya hana shi ɗaukar matakin ƙarshe kan batun.
Sai dai tsohon Kwamishinan Jihar Kano kuma Sakataren Majalisar Shura, Shehu Wada Sagagi, ya fito da wata takarda da ta ƙara jefa batun cikin ruɗani.
Takardar, mai kwanan wata 4 ga Fabrairu, 2026, ta nuna cewa Majalisar ta kammala zamanta da bincikenta kan ƙorafin da aka gabatar, sannan ta rubuta wa Gwamnan Kano domin neman lokaci da ranar da za ta gabatar masa da rahoton ƙarshe.
Abin da takardar ta bayyana shi ne, Majalisar Shura ba wai kawai ta gudanar da bincike kan ƙorafin ba ne, har ma ta kai matakin neman izinin gabatar da sakamakon binciken ga Gwamnan.
An bayyana cewa manufar gabatar da rahoton ita ce Gwamnan ya duba abin da Majalisar ta gano, sannan ya ɗauki matakin da ya dace bisa abin da rahoton ya ƙunsa.
Wannan bayani ya haifar da sabbin tambayoyi kan dalilin da ya sa Gwamnan ya ce bai karɓi rahoton ba, alhali takardar da Sakataren Majalisar ya fitar na nuna cewa an kammala binciken kuma an nemi lokacin gabatar da rahoton.
Sai dai takardar ita kaɗai ba ta tabbatar da cewa rahoton ƙarshe ya shiga hannun Gwamnan kai tsaye ba; abin da take nuna wa shi ne cewa Majalisar ta shirya gabatar da shi kuma ta nemi lokaci domin yin hakan.
Saboda haka, tambayar da jama’a ita ce, ko an gabatar da rahoton Majalisar Shura ga Gwamna Abba Kabir Yusuf ko kuwa ba a samu damar yin hakan ba?
Bayanai masu karo da juna da ɓangarorin ke bayarwa ya sa batun ke ci gaba da ɗaukar hankali, musamman saboda yana da alaƙa da zargin kalaman da suka shafi Annabi Muhammad a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwasa (SAW).


No comments