NUJ Kebbi Ta Yi Alhinin Rasuwar Tsohon Ma’aikin NAN
Daga Hadi Bawa
Ƙungiyar ’Yan Jaridu ta Ƙasa (NUJ), reshen jihar Kebbi, ta bayyana alhinin rasuwar tsohon ma’aikacin Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), Alhaji Auwalu Yusuf Birnin Kudu, wanda ya rasu yana da shekaru 57.
Marigayin ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano.
Alhaji Auwalu ya taɓa aiki a ofisoshin NAN na jihohin Kebbi, Katsina da Adamawa, inda ya gudanar da ayyukansa cikin ƙwazo da sadaukarwa.
A cikin wata sanarwa da Shugaban NUJ na Jihar Kebbi, Comrade Bello Abubakar Sarki, da Sakataren ƙungiyar, Comrade Ismail Adebayo suka sanya wa hannu, wacce TNL HAUSA ta samu, ƙungiyar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga harkar aikin jarida da kafafen yaɗa labarai.
NUJ Kebbi ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa, tsoffin abokan aikinsa da sauran waɗanda rasuwar ta shafa, tare da roƙon Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, Ya kuma bai wa iyalansa haƙurin jure wannan babban rashi.


No comments