Ni Ne Mutum Na Farko Da Zai Shiga Uku, Muddin Atiku Ya Ci Zabe - Wike
Daga Al-Amin Ciroma
A yayin da ake shirye-shiryen
dora zazzafar sanwar yakin neman zaben shekarar 2027, Ministan Babban Birnin
Tarayya, Nyesom Wike, ya furta cewa ko shakka babu, shi zai kasance mutum na
farko da zai fuskanci manyan matsaloli da kalubale, muddin har Tsohon
Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ko Peter Obi, suka yi galaba kan
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.
TNL Hausa ta ruwaito cewa Wike ya yi wannan furucin ne a yayin
da yake zantawa da manema labarai a birnin Fatakwal ta Jihar Ribas, inda ya ce;
fito-na-fiton da yake yi da ‘yan adawar APC, ya sanya shi zama babbar barazana
gare su.
Ya kara da cewa duk da yana
sane da matsalar da salon siyasarsa ka iya fadawa ciki, amma bai taba yin
nadamar goyon bayan Tinubu ba.
Mista Wike ya ce, ya
fuskanci suka da yatsine saboda yadda ya mara wa Shugaba Tinubu baya, amma a
cewarsa, hakan, ko kadan, ba ta sanyaya ma sa gwiwa ba.



No comments