Muna Jiran Mu Ga Waɗanda Za Su Tallata Mana Tinubu -Farfesa Usman Yusuf
Daga Hadi Bawa
Ƙwararren Likita, Farfesa Usman Yusuf ya soki Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, wadda Sanata Abdulaziz Yari zai jagoranta, yana mai cewa ’yan Nijeriya suna jiran ganin waɗanda za su fito su tallata gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.
A wata hira da ya yi da Symfoni TV, Yusuf ya nuna shakku kan tasirin Kwamitin, yana mai cewa gwamnati za ta dogara ne da ’yan siyasa, malaman addini, mawaƙa da ’yan fim wajen neman goyon bayan jama’a.
Yusuf ya ce naɗin Yari na iya kasancewa dabara ce ta siyasa, amma ya tambayi irin saƙon da zai kai wa mutanen Arewa, musamman kasancewar yankin ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar Tinubu a zaɓen 2023.
Ya ce yanzu jama’a za su tambayi irin ribar da suka samu daga gwamnati, tare da kwatanta halin da jihohin Arewa suke ciki da wurare kamar Legas.
Ya kuma ce matsalar tsaro, tsadar rayuwa, talauci da yunwa na daga cikin abubuwan da za su yi tasiri a zaɓen 2027.
TNL Hausa ta jiwo Yusuf yana tambayar cewa abin da Yari zai gaya wa mutanen Zamfara kan matsalar tsaro, yana mai cewa jihar tana da muhimmanci a gare shi saboda ya yi karatu a Gusau, kuma ya san yanayin jihar tun kafin matsalolin tsaro su tsananta.
Farfesa Yusuf ya kuma soki yadda wasu ’yan siyasa ke amfani da alƙaluman tattalin arziƙi da nasarorin gwamnati ba tare da la’akari da halin da talakawa suke ciki ba.
Ya kuma yi tambaya kan ko yawan gwamnoni, ’yan majalisa da sauran manyan ’yan siyasa da aka saka cikin majalisar yaƙin neman zaɓen zai isa ya tabbatar wa APC da nasara.
Yusuf ya ce abin da ya faru a Jihar Osun ya kamata ya zama darasi ga APC, domin yawan manyan ’yan siyasa ba shi ne ke tabbatar da samun ƙuri’un jama’a ba.
Ya ce yanzu yana jiran ganin yadda Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC za ta fuskanci jama’a da hujjojin da za su sa su sake zaɓar Tinubu a 2027, yana mai cewa: “Muna jira. Mutane suna jiran su cikin haƙuri.”


No comments