Breaking News

Masari Ya Nemi Malamai Su Ƙarfafa Mata Wajen Shiga Siyasa

Daga Hadi Bawa 

Babban mashawarci na musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya buƙaci malaman addinin Musulunci mata su ƙara miƙewa tsaye wejen ba da gudunmawar wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa mata su tsunduma cikin harkokin siyasa don a dama da su.

Masari ya bayyana haka ne a Kaduna a lokacin da yake ganawa da wasu manyan malaman addinin Musulunci mata daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya, kamar yadda jaridar Katsina City News ta ruwaito.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin ƙarfafa shigar mata cikin harkokin siyasa, inganta haɗin kan al’umma, da kuma ƙara fahimtar manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman shirin sabunta fata na Renewed Hope.

A yayin taron, an tattauna muhimmiyar rawar da malaman addini mata za su iya takawa wajen wayar da kan jama’a, ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai, da kuma ƙara ba mata damar taka rawar gani a harkokin siyasa da ci gaban ƙasa.

Masari ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen samar da kyakkyawar fahimta da haɗin kan al’umma, musamman a yankin Arewacin Najeriya.
TNL HAUSA ta gano cewa ganawar ta kasance wata dama ta musayar ra’ayoyi kan yadda mata, musamman malaman addini, za su ƙara bayar da gudunmawa wajen siyasa, ci gaban al’umma da tallafawa wajen wayar da kan jama'a a kan manufofin gwamnati.

No comments