Kuskuren Saira Movies Na Rasuwar Jaruman Fim Ɗin 'Labarina'
Ya zuwa yanzu dai rahotanni sun nuna cewa jarumai na shirin 'Labarina' wanda kamfanin Saira Movies ke shiryawa, guda Huɗu ne suka rasu. Saɓanin wata sanarwar da Babban Jami'i kuma Manajan Harkar Sadarwa, Ahmadu Nagudu ya shelanta.
Jaridar TNL HAUSA ta ruwaito cewa jarumai Huɗu ne suka rasu, waɗanda suka da haɗa da Saratu Giɗaɗo (Hajiya Babba), wadda ta rasu ranar 9 ga Afrilu, 2024, Umar Maikuɗi Cashman, ya rasu ranar 21 ga Mayun 2025, sai Maijidda Muhammad Kontagora (Fulani) wadda ta rasu ranar 25 ga Disambar 2025 da kuma Zainab Abdullahi - Xee Diamond (Maman Bin Ako), wadda ta rasu ranar 7 ga Satumbar 2026.
Sai dai cikin wata sanarwar da Manajan Labarai na kamfanin Saira Movie, Ahmad Nagudu ya wallafa, jam'in ya ce, jarumai Uku ne suka rasu, waɗanda suka haɗa da Umar Maikuɗi Cashman, Maijidda Muhammad Kontagora da Zainab Abdullahi Zee Diamond.
Sanarwar da TNL HAUSA ta ɗauko daga shafin na Saira Movies a dandalin Facebook ta ce:
JARUMAN SAIRA MOVIES UKU DA SUKA RASU
Ahmad Nagudu, Media Manager na Saira Movies, ya bayyana jerin jarumai uku da suka rasu, waɗanda suka taka rawa a masana'antar shirya fina-finan Hausa.
Jaruman sun haɗa da Umar Maikudi Cashman, Maijidda Muhammad Kontagora, wadda aka fi sani da Fulani, da kuma Zainab Abdullahi (Diamond), wadda aka fi sani da Talatuwa Maman Bintalo a cikin shirin Labarina.
Umar Maikudi Cashman ya rasu a ranar Laraba da dare, 21 ga watan Mayun shekarar 2025, a Zariya. An yi jana'izarsa a Zariya washegari, Alhamis da safe.
A ranar Alhamis, 25 ga watan Disambar 2025, Maijidda Muhammad Kontagora, wadda aka fi sani da Fulani, ta rasu da yamma a wani asibiti da ke Sokoto.
An yi jana'izarta a garinsu na Kontagora bayan Sallar Juma'a, a kofar Fadar Sarkin Sudan na Kontagora.
Haka kuma, Zainab Abdullahi (Diamond), wadda aka fi sani da Talatuwa Maman Bintalo a cikin shirin Labarina, ta rasu a ranar Litinin da asuba, 7 ga watan Satumbar 2026, a Zariya bayan fama da doguwar jinya.
An yi jana'izarta a Zariya a ranar da ta rasu.
Allah Ya jiƙan su da rahamarSa, Ya gafarta musu kura-kuransu, Ya sa Aljanna ce makomarsu baki ɗaya.


No comments