Kun San Waɗanda Za Su Jagoranci Sabuwar Ƙungiyar Yi Wa Tinubu Kamfen A Arewa?
Daga Hadi Bawa
Manyan ’yan siyasar Arewa, ciki har da tsofaffin gwamnoni da sanatoci masu ci da waɗanda suka taɓa riƙe muƙamai, sun kammala shirye-shiryen kafa wata ƙungiya da za ta tattara goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
TNL HAUSA ta jiwo cewa, ƙungiyar, mai suna Arewa for Asiwaju (A4A), za ta kasance wata dandalin haɗa kan ’yan siyasar Arewa domin gudanar da ayyukan wayar da kai da tattara magoya baya a jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ana sa ran ƙaddamar da ƙungiyar a hukumance a Abuja cikin ’yan kwanaki masu zuwa, kafin a gudanar da bukukuwan ƙaddamar da rassanta na shiyyoyi da jihohi.
Tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Sanata Ibrahim Shekarau ne aka zaɓo domin zama shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar.
Tsohon gwamnan Yobe kuma Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Sanata Ibrahim Geidam, da tsohon gwamnan Plateau, Sanata Simon Bako Lalong, za su kasance mataimakan shugaban kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin amintattun, wanda zai ƙunshi mutane 14, sun haɗa da Ibrahim Kabir Masari, Joshua Dariye, Buba Marwa, Aliyu Wamakko, Isa Yuguda, Jolly Nyame, Atiku Bagudu, Yahaya Bello, Aishatu Dukku, Binta Ibrahim da Mohammed Badaru Abubakar. Badaru, tsohon gwamnan Jigawa kuma Ministan Tsaro na yanzu, shi ne aka zaɓo domin zama sakataren kwamitin tare da jagorantar babban daraktan ƙungiyar na ƙasa.
A tsarin ƙungiyar, Badaru zai kula da ayyukanta a jihohin Arewa 19 da Abuja, yayin da tsohon gwamnan Katsina, Ibrahim Shema, zai kasance mataimakin mai gudanar da ayyukan Arewa maso Yamma; Yahaya Bello ya jagoranci Arewa ta Tsakiya, sannan Abdulrazaq Namdas ya jagoranci Arewa maso Gabas.
Haka kuma, an tsara daraktoci daban-daban da za su kula da harkokin kuɗi, yaɗa labarai, wayar da kai, matasa, mata, addinai, ƙungiyoyin farar hula, ’yan majalisa, bincike da dabarun yaƙin neman zaɓe, fasahar sadarwa da sauran fannoni.
Ƙungiyar ta ce an kuma tsayar da masu kula da rassanta a matakin jihohi da ƙananan hukumomi a Arewa 19 da Abuja, inda aka haɗa tsofaffin da masu riƙe da muƙaman siyasa domin tafiyar da ayyukan tattara jama’a.
Ta bayyana cewa an tsara wannan tsari ne domin samar da ingantacciyar hanyar haɗa kan al’ummar Arewa wajen tallafa wa Tinubu gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, a daidai lokacin da jam’iyyar APC mai mulki da jam’iyyun adawa ke ta ƙoƙarin shirye-shiryensu na fafe gora kafin ranar tafiya.


No comments