Ku Gane Gaskiyar Lamarin Kamfanin Siminti, KEPYO Ta Gayawa ADC Ta Kebbi
Daga Najeeb Sani
Kungiyar matasan Kebbi masu kishin kasa (KEPYO) ta soki jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen Jihar Kebbi kan ikirarinta da ta yi game da yarjejeniyar saka hannun jari da gwamnatin jihar ta kulla da kamfanin MSM Cement Limited, inda ta bukace ta da ta gane gaskiyar lamarin kafin ta yanke hukunci kan aikin.
Kakakin KEPYO, Comrade Hamisu Sani, ya bayyana matsayin kungiyar a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, a matsayin martani ga wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben ADC na Jihar Kebbi ya fitar mai taken, “Ina Kamfanin Simintin Da Kuka Sa Hannu Akai?”
Sani ya ce ADC ta karkatar da gaskiyar yarjejeniyar ta hanyar gabatar da Memorandum na fahimtar juna (MoU) na shirin kafa kamfanin siminti, kamar yadda gwamnatin jihar ta kaddamar da wata kammamacciyar masana'anta.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka kulla a watan Maris na shekarar 2025 tsakanin Gwamnatin Jihar Kebbi da kamfanin MSM Cement Limited, yarjejeniya ce ta fahimtar juna (MoU) domin gina sabon kamfanin siminti mai karfin samar da tan miliyan uku a duk shekara, ba kaddamar da wata masana'anta da ke aiki ba.
A cewarsa, wannan bambancin yana da matukar muhimmanci saboda aikin zuba jari ne na kamfanin mai zaman kansa, inda mai zuba jari ne ke da alhakin gina masana'antar, yayin da rawar da gwamnatin jihar za ta taka shi ne kawai samar da yanayi mai kyau.
Ya ce bayanai da ke shafin intanet sun nuna cewa ana sa ran za a aiwatar da aikin a matakai, inda ake sa ran matakin farko zai fara samar da siminti a kusa da shekarar 2027.
Don haka Sani ya kalubalanci jam'iyyar ADC da ta gina suka da sukar ta kan sahihan bayanai, alkawuran kwangila da kuma ainihin jadawalin lokaci na zuba jarin, maimakon daukar rashin kammala masana'antar a matsayin hujjar cewa aikin ya bace.
Ya ce KEPYO tana goyon bayan a yi rikon amana, amma ta dage cewa sukar siyasa dole ne ta ginu a kan ingantattun gaskiya da cikakken mahallin lamarin.


No comments