Jirgin Sama Ya Yi Saukar Gaggawa A Saudiyya Bayan Da Matuƙan Suka Kaure Da Faɗa
Daga Sambo Richifa, kano
Wasu matukan jirgin sama sun kaure da fada a tsakanin su saka makon sabanin ra'ayi da suka samu. An ruwaito cewa faɗan dai ya ɓarke a tsakanin matukan jirgin fasinja ne Jim kadan da ta sowarsu daga Dubai zuwa Tel Aviv a lokacin aka aika da lambar gargaɗin yiwuwar yin garkuwa da jirgi, kafin daga bisani jirgin ya sauka a Saudiyya kamar yadda Jaridar Isra’ila Ynet ta ruwaito, kuma Jaridan TNL Hausa ta yi na zarin labarin yadda lamarin ya faru.
Jirgin dai yana shirin sauka ne a filin jirgin saman Ben Gurion, kuma yana ɗauke da fasinjoji 174. Jirgin ya kuma aika da siginar din gaggawa na ɗan lokaci
Sannan sai aka kunna lambar da ke nuna yiwuwar yin garkuwa da jirgin, a inda nan take rikici ya ɓarke a cikin ɗakin matukan jirgin.
Daga bisani jirgin ya sauka a filin jirgin saman Tabuk na Saudiyya.
Tun da farko dai Kimanin mintuna 90 bayan tashinsa, yayin da jirgin ke shiga sararin samaniyar Jordan, ya aika da lambar “7700”, wadda ake amfani da ita a duniya wajen nuna wata babbar matsalar gaggawa.
A kusan lokaci guda, jirgin ya sauya hanya, ya koma cikin sararin samaniyar Saudiyya, sannan ya fara shawagi a ƙasa a kan ƙasar, a cewar rahoton wanda TNL Hausa ta ci Karo da shi
kafin dai ya yi saukan gaggawar a kasar Saudiya an ga jirgin ya fara tafiya zuwa kudu, sannan kuma ya juya zuwa yamma, yayin da yake ci gaba da kasancewa cikin sararin samaniyar Saudiyya, kafin daga bisani ya sauka a ƙasar.
Sai dai daaga bisani tashar Channel 12 ta Isra’ila ta ce al’amarin bai yi kama da wata matsalar tsaro ba, kuma hukumomi na binciken ko an kunna siginar gaggawar ne bisa kuskure sakamakon wata gardama tsakanin matukin jirgin da mataimakinsa.
Tashar ta ce ma’aikatan jirgin sun haɗa da wani matukin jirgi ɗan Rasha da mataimakin matukin jirgi ɗan Ukraine
Hukumomin Isra’ila dai sun ce za su tura wani jirgin daga Dubai zuwa Saudiyya domin dawo da fasinjojin Isra’ila da ke cikin jirgin
Wasu manyan jami’an masana’antar sufurin jiragen sama ta Isra’ila sun ce har yanzu ba a kawar da zargin cewa lamarin na da alaƙa da tsaro ba, kamar yadda Ynet ta ruwaito.
A cewar wani bincike na farko da jami’an suka ambata, ana zargin ɗaya daga cikin matukan jirgin da “ƙoƙarin haddasa hatsarin jirgin,” yayin da ɗayan matukin ya yi nasarar dakile yunƙurin tare da taimakon wasu fasinjojin Isra’ila.
Ofishin Firaministan Isra’ila ya ce lamarin yana “ƙarƙashin iko”, tare da cewa “ana amfani da dukkan hanyoyin da ake da su yanzu domin tabbatar da an dawo da fasinjojin Isra’ila cikin aminci zuwa Isra’ila.”


No comments