Breaking News

Jami'ar Gombe Ta Yi Wa Gwarzuwar Gasar Karatun Alƙur’ani Alƙawarin Aiki

Daga Hadi Bawa

Jami’ar jihar Gombe (GSU), ta yi wa wata ɗalibarta mai shekaru 19, Maryam Ibrahim Ɗan’Azumi da  ta lashe gasar karatun Alƙur'ani ta duniya a Saudiyya, alƙawarin ba ta aiki bayan kammala karatunta.

TNL HAUSA ta lura cewa Maryam, wadda ke karanta Physics Education a Jami’ar, ta samu wannan dama ne bayan da ta lashe wata gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa da aka yi a Saudiyya.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Sani Ahmed Yauta ne ya bayyana wannan alƙawarin yayin da yake taya Maryam murnar nasarar da ta samu.

Farfesa Yauta ya ce Jami’ar jihar Gombe za ta ci gaba da tallafa wa Maryam har zuwa lokacin da za ta kammala karatun digirinta.

Ya bayyana cewa bayan kammala karatunta, za a ba Maryam damar yin aiki a Jami’ar domin ta ba da gudunmawarta ga ci gaban makarantar.

A cewarsa, hakan zai kuma ba ta damar zama abar koyi da ƙarfafa gwiwar sauran matasa wajen neman ilimi da kuma shiga harkokin da za su amfani al’umma.

Daga bisani ya yi wa Maryam fatan Allah Ya ƙara mata ilimi, nasara da ɗaukaka, tare da ci gaba da ba ta damar cimma burinta na rayuwa.

No comments