Breaking News

INEC Ta Tabbatar Da ’Yan Takarar Shugaban Ƙasa 18

Daga Aliyu Saleh

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da cikakken jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa 18 da mataimakansu na zaɓen gama-gari da za a gudanar ranar 16/01/2027.

Jaridar TNL HAUSA ta rawaito cewa jam’iyyun siyasa 18 ne suka gabatar da ’yan takararsu na kujerar shugaban ƙasa a jerin sunayen da Hukumar ta fitar.

A wata sanarwa da Sakatariyar INEC, Rose Oriaran-Anthony ta raba wa manema labarai, jerin sunayen ya ƙunshi sunan Shugaban Ƙasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, na jam’iyyar APC; tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar ADC; tsohon Gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, na jam’iyyar NDC; da ɗan takarar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore.

Sauran fitattun ’yan takarar da ke cikin jerin sunayen sun haɗa da Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, na jam’iyyar APM; tsohon Gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, na jam’iyyar PRP; Adewole Adebayo na jam’iyyar SDP; Sandy Ojang Onor na jam’iyyar PDP; da Sunday Chibuizu Okereke na jam’iyyar Labour Party.

Hukumar ta kuma bayyana sunayen mata biyu da ke takarar shugabancin ƙasa, wato Ada Elizabeth Frederick Okwori ta jam’iyyar NDP da Nkem Esther Okereke ta jam’iyyar NRM.

A jimlace, maza 16 ne ke hanƙoron kai wa ga kujerar shugaban ƙasa a zaɓen da ke tafe, yayin da mata biyu ne kacal ke cikin ’yan takarar 18 da INEC ta amince da sunayensu.

Tuni dai jerin sunayen nan suka fara tayar da muhawara a tsakanin 'yan Najeriya, yayin da hankali ya fara karkata kan wannan gudun ya da ƙanin wani da aka fara.

No comments