Breaking News

Gwamnatin Sokoto Fara Binciken Kalaman Sheikh Lukuwa

Daga Shafii Haruna

Rahotanni daga Jihar Sokoto sun ce, gwamnatin jihar ta kafa kwamitin binciken matakin da shari'a ya tanada a kan kalaman Sheikh Musa Lukuwa.

TNL HAUSA ta ruwaito cewa, a cikin wata takarda da Daraktan Yaɗa Labarai na ofishin Gwamnan, Mallam Abubakar ya sanya wa hannu, ta nuna cewa Mallam Yahya na Mallam Ɓoyi (Sarkin Malamai) shi zai jagoranci kwamitin na musamman game da wannan lamarin.
An dai ba wa kwamitin damar gudanar da bincike yadda ya dace wajen bayyana hanyoyin magance matsalar furucin da Malam Lukuwa ya saba yi.

No comments