Gombe 2027: Tsohon Ma’ajin Kasa Na PDP Ya Yi Alkawarin Mara Wa Jamilu Gwamna Baya
Daga Najeeb Sani, Gombe
Tsohon Ma’ajin Kasa na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hon. Ahmed Yayari, ya yi alkawarin zai yi aiki tukuru wajen ganin Dr Jamilu Isyaku Gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya zamo gwamnan jihar Gombe na gaba a babban zaben 2027.
Yayari ya bayyana haka ne a Gombe lokacin da tawagar manyan ‘yan jam’iyyar APC daga Tumfure, Wuro Bobbo, Wuro Bawa, NTA da sauran sassan Karamar Hukumar Akko suka kai masa ziyara bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kwanan nan.
Tawagar ta APC, yayin ziyarar, ta roki Yayari da ya shiga jam’iyyar, inda suka bayyana shi a matsayin kadara ta siyasa da kuma mutumin da ke da gogewa wanda kasancewarsa zai karfafa jam’iyyar gabanin zaben 2027.
Musamman sun ambaci gogewarsa a matsayin tsohon Daraktan yakin neman zabe na tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, a matsayin babbar kadara ga jam’iyyar.
Tawagar ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwa cewa sauya shekar Yayari da goyon bayan da zai ba Jamilu zai kara karfafa damar APC a zaben gwamna na 2027.
Suka kara da cewa yankunan da suke wakilta suna da rumfunan zabe 24, inda suka jaddada cewa goyon bayansu gaba daya zai iya ba da gudummawa mai yawa ga nasarar jam’iyyar a zabe.
A nasa martanin, Yayari ya bayyana shirinsa na tallafawa burin Jamilu na zama gwamna, inda ya ce: “Na shirya in yi aiki tukuru wajen ganin nasar Jamilu Gwamna a matsayin gwamnan jihar Gombe na gaba.”


No comments