Breaking News

Gombe 2027: Tinka Ya Karbi Jigo a APC, Babawo Dukku a Jam'iyyar ADC


Daga Najeeb Sani 

Wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Gombe kuma tsohon dan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada, Hon. Babawo Dukku, ya fice daga APC ya koma jam'iyyar African Democratic Congress (ADC).

Hon. Dukku an karbe shi a hukumance a cikin jam'iyyar ADC ne ta hannun dan takarar gwamna na jam'iyyar, Dr. Bala Bello Tinka, a garin Dukku.

Dukku yace ya bar APC ne bayan shawarwari da tuntuba mai zurfi da ya yi da iyalansa, magoya bayansa da kuma dattawan siyasa a Dukku da Jihar Gombe baki daya.

Ya bayyana cewa matakin da ya dauka na komawa ADC da hada karfi da Dr. Bala Bello Tinka ya samo asali ne daga kwakkwaran imaninsa cewa ADC ce kadai jam'iyyar da za ta iya ceto Jihar Gombe da kuma samar da shugabanci na gaskiya gabanin zaben 2027.

"Bayan shawarwari masu zurfi, na yanke shawarar yin murabus daga APC kuma na koma ADC. Ina da yakini da hangen nesa da salon jagorancin Dr. Bala Tinka. Tare da magoya bayana, zamu yi aiki tukuru don ganin nasarar ADC a Dukku, Gombe da Najeriya baki daya," inji Dukku.

Hon. Dukku ya kuma bayyana cewa zai rusa dukkan tsarin siyasarsa da ke Dukku ya hada da na jam'iyyar ADC nan take, tare da yin kira ga magoya bayansa da su hada hannu domin gina sabuwar Jihar Gombe.

Da yake tarbar sa, Dr. Bala Bello Tinka ya nuna farin cikinsa matuka kan wannan ci gaba, inda ya bayyana Hon. Dukku a matsayin dan siyasa mai tushe a kasa kuma gogaggen dan siyasa wanda shigowarsa zai kara karfin ADC matuka a Dukku/Nafada da kuma Gombe ta Arewa baki daya.

No comments