Farfesa Bukar Maina Ya Zama Malami A Jami’ar Sussex, Birtaniya
Daga Hadi Bawa
Fitaccen masanin ilimin ƙwaƙwalwa ɗan asalin Birtaniya da Najeriya, Farfesa Mahmoud Bukar Maina, haifaffen Nguru a jihar Yobe, ya samu sabon muƙami na a Jami’ar Sussex da ke ƙasar Birtaniya.
Jami’ar Sussex ita ce makarantar da Farfesa Maina ya yi karatunsa tare da gina ƙwarewarsa a fannin ilimin ƙwaƙwalwa, lamarin da ya sa sabon muƙamin ya zama wani muhimmin ci gaba a rayuwarsa ta fannin ilimi da binciken kimiyya.
A halin yanzu, Farfesa Maina babban Malami ne a fannin Neuroscience, kuma wanda ya kafa tare da jagorantar Cibiyar Nazari da Horar da Kimiyyar Biomedical (BioRTC) ta Jami’ar Jihar Yobe.
Ya yi fice, sannan bincikensa ya kai matakin ƙasa da ƙasa, musamman kan dangantakar asali da cututtukan Alzheimer, Dementia da Tauopathies da kuma hanyoyin da cututtukan ke tasiri ga jikin ɗan Adam.
Bincikensa ya fi mayar da hankali kan al’ummomin da ba a cika gano su ba a binciken kimiyya.
Tun daga shekarar 2022, cibiyar BioRTC da yake jagoranta ta horas da sama da matasa 300 masu tasowa a fannin kimiyya daga ƙasashen Afirka, musamman kan ilimin ƙwaƙwalwa, amfani da hotunan kimiyya wajen bincike (bioimaging) da kuma tsarin gudanar da bincike na kimiyya a bayyane.
Baya ga bincike da koyarwa, Farfesa Maina ya taka rawa wajen bunƙasa wayar da kan jama’a game da kimiyya.
Ya kafa TReND in Africa a Birtaniya, Science Communication Hub Nigeria da African Science Literacy Network, waɗanda ayyukansu suka kai ga miliyoyin mutane a sama da ƙasashen Afirka 10.
A fannin hidimar gwamnati kuma, a halin yanzu Farfesa Maina yana aiki ne a matsayin Babban Mai Ba Gwamnan Jihar Yobe, Mala Buni, shawara kan kimiyya, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire.
Farfesa Maina ya samu lambobin yabo da karramawa da dama daga ƙungiyoyi da cibiyoyin ƙasa da ƙasa, ciki har da Royal Society of Biology, ALBA-FKNE, New England BioLabs da Jami’ar Sussex.
A ranar 11 ga Yuli, 2025, Majalisar Masarautar Damaturu ta kuma naɗa shi sarautar gargajiya ta Shettima Ilumuye na Damaturu, wadda ke nufin mai kula da ilimi da wayar da kan jama’a.


No comments