Breaking News

EFCC Ta Sa Maina Cikin Waɗanda Take Nema Ruwa A Jallo

Daga Hadi Bawa 

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC, ta sanya tsohon shugaban Pension Reform Task Team, Abdulrasheed Abdullahi Maina, cikin mutanen da take nema ruwa a jallo.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026, EFCC ta ce tana neman Maina mai shekaru 61 bisa zargin karɓar kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Hukumar ta kuma yi kira ga duk wani mutum da ke da masaniya kan inda Maina yake da ya sanar da ita, ko kuma ya tuntuɓi wata hukumar tsaro domin taimakawa wajen gano shi.

Maina ya taɓa fuskantar shari’a a gaban kotu kan zargin karkatar da kuɗaɗen fansho.

A watan Nuwamba na shekarar 2021, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗe da kuma halatta kuɗin haram, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari.

Abin tambaya a nan shi ne, ya gama wa'adinsa na gidan yarin ne, ko kuma ya fita ta ɓarauniyar hanya ce?

No comments