Breaking News

Daliban Arewa Sun Yi Allah-Wadai Da Dakatar Da Dalibin Aji 5 Na MAU

Na Najeeb Sani

Ƙungiyar Daliban Arewacin Najeriya (Association of Northern Nigerian Students - ANNS), ta yi Allah-wadai da dakatarwar da ba ta da lokacin Æ™arewa da aka yi wa dalibin Aji 5 na Jami’ar Modibbo Adama (MAU), Yola, Jihar Adamawa, Promise Bitrus, inda ta bayyana shi a matsayin hari kan hakkin É—alibai na tsari.

A cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Adamu, ya sanya wa hannu kuma ya aika wa wakilinmu, ANNS ta ce an dakatar da Bitrus ne kawai saboda shirya zanga-zangar lumana domin bayyana korafe-korafen da ke shafar É—alibai a harabar jami’ar.

Ƙungiyar É—alibai ta kuma yi Allah-wadai da “dakatarwar ayyukan dandalin É—alibai na Arewacin Najeriya - GAMJI Students a MAU ba tare da iyaka ba,” wadda ta bayyana a matsayin muhimmin dandali na haÉ—in kai, jin daÉ—in É—alibai, da muhawara ta ilimi ga É—alibai Arewa a jami’ar.

“ANNS na ganin wannan mataki a matsayin hari kai tsaye kan haÆ™oÆ™in ‘yancin faÉ—ar albarkacin baki, taro na lumana, da Æ™ungiyanci kamar yadda Sashi na 39 da 40 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.
  
ANNS ta ba Gudanarwar Jami’ar Modibbo Adama da Shugaban Jami’ar sa’o’i 72 daga yanzu domin su É—auki matakai uku da suka hada da; dage dakatarwar da ba ta da lokacin Æ™arewa da aka yi wa Promise Bitrus ba tare da wani sharadi ba. 

Ta kuma bukaci a mayar da ayyukan GAMJI Students a MAU, da kuma ba da dama a bi tsari wajen warware duk wata matsalar shugabanci ta ciki. 

Sannan kungiyar ta bukaci tsayawa da ƙarin tsoratawa, zalunta, ko azabtarwa ga ɗalibai masu gudanar da zanga-zanga ta lumana da doka ta tanada.

Ƙungiyar ta yi gargadin cewa idan ba a bi wadannan sharudda ba cikin sa’o’i 72 ba, za ta tattara dukkan É—alibai na Arewacin Najeriya a faÉ—in Æ™asa, tare da sauran Æ™ungiyoyi masu alaÆ™a, domin gudanar da babbar zanga-zangar lumana don neman adalci.

ANNS ta ce ta himmatu wajen zaman lafiya, tattaunawa, da bin doka, kuma ta roÆ™i Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta yi aiki don muradun É—alibai da kwanciyar hankalin makarantar.

Ƙungiyar ta kuma roÆ™i Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa - NUC, NANS, da sauran masu ruwa da tsaki da su shiga tsakani domin tabbatar da an yi adalci.

A cewar ANNS, jagorancin ɗalibai na wanzuwa ne domin zama gada tsakanin Hukumar Makaranta da ɗalibai, inda ta ƙara da cewa azabtar da shugabannin ɗalibai masu magana ya kafa mummunan tarihi.

No comments