DA ƊUMI-ƊUMI: Dakarun Houthi Sun Karɓi Ragamar Yankin Bahar Maliya A Yemen
Rahotanni sun ce yaƙi tsakanin ƙasar Saudiyya da Yemen da ya ƙi ci, ya ƙi cinye wa na ci gaba da ɗaukar sabon salo.
Jaridar TNL HAUSA ta ruwaito cewa a yanzu ƙungiyar Houthi ta AnsaralAllah ta karɓi ragamar tekun Bahar Maliya. Wanda ke nuna ci gaba da samun nasara da take yi a yaƙin.
Idan dai ba a manta ba, a shekarar 2023 ne Saudiyya ta amince da bai wa AnsarAllah (Houthis) cikakken iko da mulkin Yemen. An riga an cimma yarjejeniyar, kuma abin da ya rage kawai shi ne a sanya hannu a hukumance.
Sai dai bayan da AnsarAllah ta kai wa Isra’ila hari domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa, Saudiyya ta yanke shawarar ba za ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba.
Daga baya, Saudiyya ta nemi AnsarAllah da kada su kai hari kan Isra’ila ko jiragen ruwa masu alaƙa da Isra’ila a Tekun Bahar Maliya. A madadin haka, AnsarAllah za ta samu cikakken iko da mulkin Yemen, tare da zuba jari a tattalin arzikinta.
Amma AnsarAllah ta ƙi, tana cewa: “Ba za mu taɓa yin watsi da Falasɗinu ba.”


No comments