Breaking News

APC Ta Lashe Kujeru 3 A Kano, Bauchi Da Gombe

Daga Hadi Bawa 

Jam'iyyar APC da ke mulki ta lashe kujeru uku da aka fafata a zaɓukan cike gurbi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gudanar a jihohin Kano, Bauchi da Gombe.

TNL HAUSA ta ruwaito cewa, zaɓukan sun gudana ne a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta, inda INEC ta gudanar da aikin zaɓe domin samar da waɗanda za su maye gurbin kujerun da suka kasance babu kowa.

A Kano, ɗan takarar APC, Hussaini Yusuf Datti, ya lashe kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Dawakin Kudu/Warawa, bayan ya samu ƙuri’u 22,890.

Jam’iyyar PRP ta zo ta biyu da ƙuri’u 270, yayin da PDP ta samu 108. APP ta samu ƙuri’u 53, sannan LP ta samu ƙuri’u 39.

A Bauchi kuma, ɗan takarar APC, Yakubu Ali, ya lashe kujerar majalisar dokokin jihar mai wakiltar Disina, inda ya samu ƙuri’u 5,846, yayin da ɗan takarar APM ya zo na biyu da ƙuri’u 5,225. PRP ta samu ƙuri’u 3,701.

A jihar Gombe kuwa, ɗan takarar APC, Kallamu Usman Mai Jama’a, ya lashe kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, bayan ya samu ƙuri’u 41,121. LP ta samu 3,553, yayin da APM ta samu 872.

INEC ta gudanar da zaɓukan cike gurbin ne domin maye gurbin kujerun majalisun dokoki da suka zama babu kowa a mazaɓun da abin ya shafa.

An gudanar da zaɓukan ne domin cike guraben kujerun da suka samu tangarda a majalisun dokoki, inda kujera ɗaya ta kasance ta majalisar dokokin tarayya, yayin da sauran kujeru huɗu suka kasance na majalisun dokokin jihohi.

Sakamakon da aka bayyana ya nuna cewa APC ce ta samu rinjaye a mafi yawan kujerun da aka fafata, inda ‘yan takararta suka samu nasarar lashe huɗu daga cikin kujeru biyar.

Sai dai jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta samu nasarar lashe kujera ɗaya daga cikin kujerun da aka fafata a jihar Bauchi.

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun shaida wa TNL HAUSA cewa, wannan sakamakon wata manuniya ce a kan babban zaɓen da ke tafe a shekara mai zuwa.

No comments