Breaking News

An Karrama Marigayi Jarman Kauru Da Lambar Yabo

Daga Yusuf Zubairu Kauru 

Marigayi Jarman Kauru, Malam Suleiman Lawal, kuma tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, ya samu lambar yabo ta karramawa bayan rasuwarsa, saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi da ci gaban al’umma.

An miƙa lambar yabon ga iyalansa a ranar Asabar, 5 ga watan Satumban 2026, a Zariya.

Kafar yaɗa labaran da ta bayar da lambar ta ce ta karrama shi ne saboda irin gudunmawar da ya bayar ga al’umma, musamman a Kauru da sauran sassan Jihar Kaduna.

An haifi Malam Suleiman Lawal a Kauru a ranar 12 ga Satumban 1948. Ya yi aiki a fannin ilimi na tsawon shekaru, inda ya koyar a makarantu daban-daban, sannan ya yi aiki a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna da ke Zariya, inda daga bisani ya zama shugaban kwalejin a shekarar 1992.

Bayan ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 1998, ya ci gaba da shiga harkokin siyasa da hidimar jama’a. Ya taɓa zama Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, sannan ya yi aiki a wasu hukumomi da majalisun gudanarwa, ciki har da Hukumar Tabbatar da Daidaiton Wakilcin Jihohi a Gwamnatin Tarayya da Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

An ba shi sarautar Jarman Kauru a shekarun 1980, saboda irin gudunmawar da ya bayar ga al’ummarsa. Ya riƙe sarautar har zuwa rasuwarsa a ranar 3 ga Janairu, 2026.

An jinjina yadda marigayin ya taimaka wa marasa ƙarfi, tallafa wa ilimi, da kuma taimaka wa mutane wajen samun damar karatu da aikin yi.

Babban ɗansa, Alhaji Usman Suleiman Lawal, ya gaje shi a matsayin Jarman Kauru, wanda shi da ɗan uwansa, Alhaji Nuraddeen Suleiman Lawal ne suka karɓi lambar yabon a madadin iyalan marigayin, inda suka gode wa Jaridar Taskira  bisa karrama mahaifinsu.

No comments