An Ba Ni Cin Hancin Naira Miliyan 250 Don In Goyi Bayan Tazarcen Obasanjo -Farouq Aliyu
Daga Shafi'i Haruna
Tsohon shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilan Najeriya, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa ya ƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 250 da aka ba shi domin ya goyi bayan yunƙurin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na neman wa’adi na uku a mulki.
Aliyu ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin ‘Naija Unfiltered’, wanda aka wallafa a YouTube ranar Juma’a da jaridar The Cable ta wallafa.
TNL HAUSA ta ruwaito cewa, batun neman wa’adi na uku na Obasanjo na daga cikin manyan batutuwan da suka janyo ce-ce-ku-ce a lokacin mulkinsa, wanda ya fara daga 1999 zuwa 2007.
A watan Mayun 2006, Majalisar Dokoki ta ƙasa ta yi watsi da wani ƙudirin gyara Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da zai ba Obasanjo damar neman wa’adi na uku a jere. Duk da haka, Obasanjo ya sha musanta cewa ya taɓa neman wa’adi na uku, inda a watan Satumban 2025 ya ce bai taɓa yin irin wannan buri ba.
Sai dai Aliyu ya ce, duk da musantawar tsohon shugaban ƙasar, shirin neman wa’adi na uku ya kasance gaskiya. Ya ce a lokacin da ake tattauna batun, tsohon shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribaɗu, ya nemi ya je Abuja domin ganawa da Obasanjo.
Aliyu ya ce da farko ya ƙi amincewa da gayyatar, amma daga bisani ya amince ya je ganawar, inda ya bayyana wa Obasanjo matsayinsa na cewa yunƙurin neman wa’adi na uku ba zai yi nasara ba.
Aliyu ya ƙara da cewa wani mutum da Ribaɗu ya tura ya gana da shi ya ba shi Naira miliyan 250 domin ya goyi bayan shirin, amma ya ƙi karɓar kuɗin. Sai dai bayyana sunan mutumin da ya ba shi kuɗin ba.
Ya kuma ce Aminu Masari, wanda a lokacin yake Kakakin Majalisar Wakilai, an ba shi Naira miliyan 400 domin ya goyi bayan shirin, amma ya ƙi karɓa.
Haka kuma, ya ce Abdul Ningi, wanda yake jagoran masu rinjaye a majalisar a lokacin, shi ma an ba shi Naira miliyan 400, amma bai karɓa ba, yayin da wasu ‘yan majalisa aka ba su aƙalla Naira miliyan 50.
Tsohon shugaban marasa rinjayen ya kuma bayyana cewa marigayi Muhammadu Buhari, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da George Akume, wanda a lokacin yake Sakataren Gwamnatin Tarayya, sun taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin neman wa’adi na uku.
Ya ce waɗannan mutane na daga cikin waɗanda suka taimaka wajen hana shirin samun nasara.


No comments