Breaking News

Sarkin Kano Zai Gudanar Da Hawan Maulidi A Karon Farko

Daga Habeeba Sanda Lemu

Rahotanni daga birnin Kano sun ce, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, zai gudanar da Hawa na musamman domin Maulidin haihuwar Manzon Allah (SAW)a karo na farko, a tarihin Masarautar Kano.

TNL HAUSA ta ruwaito cewar za a fara gudanar da Hawan Maulidin tun daga fadar Sarki a  ranakun Asabar da Lahadi, inda Sarkin zai fito domin halartar bukukuwan na Maulidi.

Hawan Maulidi dai, kamar yadda aka sani, wata al’ada ce da wasu masarautun Arewacin Najeriya ke gudanarwa a ranar 12 ga Rabi’ul Awwal, domin nuna farin ciki da girmamawa ga Manzon Allah (SAW).

Wane fata za ku yi wa San-Kano?

No comments