Kotu Ta Tura Faruk Abuja Gidan Yari, Bayan Zargin Cin Zarafin Ministan Tsaro
Daga Al-Amin Ciroma
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tura fitaccen dan TikTok, Faruk Musa Muhammad, wanda aka fi sani da Faruk Abuja, gidan yari na Kuje kan zargin cin zarafin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa a dandalin yanar gizo.
TNL HAUSA ta rawaito cewa, an gurfanar da Faruk mai shekara 35 ne a gaban Mai Shari’a Obiorah Egwuatu kan tuhume-tuhume guda hudu.
Ana zargin Faruk da wallafa cewa Sojojin kasar nan da ke yaki da ta’addanci suna rasa rayukansu saboda gazawar Ministan Tsaro da shugabannin rundunonin tsaro wajen daukar matakan da suka dace, tare da wasu zarge-zarge kan mai bai wa Ministan Shawara kan Harkokin Shari’a, Aliyu Anas.
Wakilinmu ya ce, Faruk ya musanta dukkan tuhume-tuhumen, yayin da lauyansa, Abdulkadir Ahmad, ya sanar da kotun cewa yana da bukatar neman beli.
Mai Shari’a Egwuatu ya dage sauraron bukatar belin zuwa ranar 9 ga Satumba, 2026, tare da bayar da umarnin tsare Faruk a gidan Yari na Kuje har zuwa lokacin.


No comments