Breaking News

An Yi Ruguntsumi A Daura, Hannatu Musawa Ta Zama Mairamar Ƙasar Hausa

Daga Aliyu Saleh 

Masarautar Daura ta karrama wasu fitattun mata biyu ’yan Nijeriya, Mrs. Folashade Tinubu-Ojo da Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido, Hannatu Musa Musawa, da lambobin yabo na gargajiya bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma da bunƙasa al’adun Hausa.

An gudanar da bikin karramawar ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, a yayin bikin Sallar Gani ta Maulidi da ake gudanarwa a Daura, inda Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa, ya kasance cikin waɗanda suka halarci taron.
Tinubu-Ojo, wadda ita ce Iyaloja-Janar ta Nijeriya da Legas, an ba ta lambar yabo ta Jakadiyar Ƙasar Hausa, yayin da Musawa ta karɓi lambar yabo ta Mairamar Ƙasar Hausa.

Da yake bayyana farin cikinsa kan karramawar, Gwamna Raɗɗa ya ce lambobin yabon sun dace da waɗanda aka bai wa, la’akari da gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma, musamman wajen haɓaka al’adu, ƙarfafa mata da kuma tallafa wa ci gaban ƙasa.
Gwamnan ya ce bikin ya sake jaddada muhimmiyar rawar da masarautun gargajiya ke takawa wajen kare asalin al’umma, ɗabi’u da al’adun da aka gada iyaye da kakanni. 
Ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyuka na taimakawa wajen tabbatar da cewa al’adun Hausa sun ci gaba da samun muhimmin matsayi a cikin al’umma.

A madadin Gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar, Gwamna Raɗɗa ya taya waɗanda aka karrama murna, tare da yi musu fatan samun hikima da ƙarfin gwiwar ci gaba da yi wa al’umma hidima.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya ci gaba da bunƙasa Masarautar Daura da Katsina, tare da ƙarfafa cibiyoyin gargajiya domin su ci gaba da zama ginshiƙai na haɗin kai, zaman lafiya da kuma kiyaye al’adun da Hausa suka gada.

No comments